Daga Wakilinmu
Wasu fasinjojin jirgi da suka fusata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano MAKIA, da ke jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsaikon da jirgin Max Air ya yi a yayin da suke shirin zuwa Legas.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Read also: Rigimar Masarautar Kano Na Daf Da Zama Tarihi, In Ji Kwamishina Waiya
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Jirgin na kamfanin Max Air mai lamba (VM1645) wanda aka shirya zai tashi da karfe 1:00 na rana, sai aka jinkirta lokacin tashisa jirgin ba tare da an sanar da fasinjojin ba, inda suka zauna na kusan sa’o’i biyar.
Bayanai sun yi nuni da rashin isar da sako daga kamfanin ya kara dagula lamarin, wanda ya haifar da tashin hankali a ɓangaren sufurin cikin gida.




























