Daga Wakilinmu
Gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kashi 25% zuwa 35% na albashi ga ma’aikatan gwamnati a kan sauran tsare-tsare guda shida na tsarin albashin.
Read also: Gwamnatin Tarayya ta Sanar Da Juma’a a Matsayin Ranar Hutu GA Ma’aikata
Tsare-tsaren albashin sun halarda ƙarfafa tsarin albashin ma’aikata na jama’a (CONPSS), ƙarfafa bincike da
tsarin albashin makarantun haɗaka (CONRAISS) da ƙarfafa tsarin albashin ƴan sanda (CONPOSS) da ƙarfafa tsarin albashin Sojoji (CONPASS).
Sauran su ne ƙarfafa tsarin albashin al’umma na Intelligence (CONICCS) da tsarin albashin Sojoji (CONAFSS).
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Idan za a tuna, tuni waɗanda ke cikin manyan makarantun gaba da harkokin lafiya suka samu karin albashin da suka halda da Consolidated University Academic Salary Structure (CONUASS) da Consolidated Tertiary Institutions Salary Structure (CONTISS).
ga Jami’o’i.
Na manyan makarantun kimiya da fasaha da Kwalejoji na Ilimi, ya haɗar da Ƙirƙirar Makarantun Fasaha da Kwalejojin Ilimi Tsarin Ma’aikata na Albashi (CONPCASS) da Ƙarfafa Tsarin Albashi na Manyan Makarantun Ilimi (CONTEDISS).
Sashen Kiwon Lafiya ya kuma amfana ta hanyar Ƙarfafawa Likitoci wato ta tsarin albashi (CONMESS) da Tsarin albashin Sashen Lafiya (CONHESS).
Read also: Shugaba Tinubu ya Amince da Ranakun Hutun Sallah Ƙarama
Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ‘yan jaridu na Hukumar Kula da Ma’aikata da samar da Kudaden Shiga (NSIWC), Emmanuel Njoku ta ce karin albashin ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2024.
Gwamnatin tarayya ta kuma amince da karin kuɗin fansho tsakanin kashi 20% zuwa 28% na masu karɓar fansho.



























