Daga Muazu Hardawa, Bauchi
An shawarci jama’a su bayar da cikaken goyan baya domin a samu cimma nasara wajen zartas da kudirori 28 na bunkasa ilmi da aka tsara a wajen taron da gwamnatin Jihar Bauchi ta shirya domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta na tabarbarewar fannin ilmi a jihar, musamman ganin yadda aka bayyana Jihar Bauchi a matsayin Wacce ke kan gaba wajen cire yara daga makarantu.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Sakataren hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Bauchi Dokta Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilinmu a Bauchi.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Ya ce taron masu ruwa da tsaki a fanin Ilimin (Education summit) wanda ya gudana a sansanin alhazai na Bauchi kwanakin baya abin a yaba ne. In da ya ce la-shaka yin amfani da managartar shawarwari da aka tsamo mafita ne ga ci gaban al’ummar da ma jihar Bauchi Baki Daya.
Sakataran ya ce ganin yadda aka gayyaci kwararru akan harkokin inganta ilmi kuma aka tattauna, suka kuma bayar da shawarwari da suka dace alamu sun nuna an dauko hanyar gyara Kuma da akwai kyakyawan zaton za a haifar da da mai ido.
Read also: GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA SOKE TAKARDUN FILAYEN KIWO DA AKA RABAWA MANOMA A DARAZO
“Musamman yadda aka gayyaci masana daga ciki da wajen kasa domin neman mafita game da matsalar da ake fuskanta a fannin ilmi, tabbas sun nuna Idan mutane sun bayar da goyan bayan su kwalliya za ta biya kudin sabulu”, inji Dokta Abdurrahaman.
Amma idan mutane suka nuna halin ko in kuda wajen Kai yaransu makaranta da lura da tarbiyya su, to akwai damuwa. Don haka ya kamata mutane su bawa gwamnati cikaken goyan baya don gyara tarbiyyar yaran su.




























