Daga Abdu Ado
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan kasafin kudi na shekarar 2024.
Read also: Gwamnan Abba Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin 2026, na zambar N1.368 tiriliyan
Da yake jawabi yayin sanya hannu kan kasafin kudin wanda ya haura sama da Naira biliyan 437, gwamna Abba Kabir ya ce kasafin kudin zai fara aiki ne a watan Janairun shekara mai kamawa.
Ya ce an ware kaso sittin da hudu cikin dari (64%) domin aiwatar da manyan ayyuka, yayin da ayyukan yau da kullum aka ware musu kaso talatin da shida(36%) dari na kasafin kudin.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu

Gwamna ya ce kasafin kudin zai kawo ci gaba ta fuskar Ilimi da lafiya da noma da ayyukan raya kasa tare da bunkasa tattalin arzikin alumar jihar Kano.
Read also: “Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
A nasa bangaren shugaban majalisar dokoki ta jiha Alh. Jibril Ismaila Falgore ya ce al’umur jihar Kano zasu ga sauye-sauye masu ma’ana a fadin jihar nan.




























