Connect with us

Hi, what are you looking for?

WASANNI

Ronaldo Ya Ce Yana Da Tabbas Na Kara Cin kwallaye a 2023

Chirstiano
Chirstiano

Daga Abdu Ado

Ronaldo ya ci kwallonsa ta 50 a bana a lokacin da kungiyar Al Nassr take fafatawa da Al Shabab inda aka tashi 5-2 a gasar cin Kofin Sarkin Saudiyya.

Christiano Ronaldo ya ce har yanzu akwai sauran kwallayen da zai ci a bana bayan ya ci kwallonsa ta 50 a 2023.

Ya bayyana haka ne bayan kungiyarsa ta Al Nassr ta ci Al Shabab 5-2 a gasar Cin Kofin Sarkin Saudiyya.

Tsohon dan wasan na Manchester United da Real Madrid ya ci kwallon a kusa da kusa da kafarsa ta dama a minti na 74.

“Babban nasara kuma ina farin cikin sanar da cin kwallota ta 50 a 2023,” kamar yadda dan wasan na Portugal mai shekara 38 ya rubuta a shafinsa na Instagram bayan kwallon tasa ta taimaka wa kulob din ya kai zagayen kusa da na karshe a ranar Litinin.

“Ina godiya da irin goyon bayan da na samu daga ‘yan kungiyata da magoya bayana da kuma iyalaina! Akwai sauran damar cin wasu a bana.”

Dan wasan ya ci akalla kwallo daya a kusan duka wasan da ya buga wa kungiyar ta Al Nassr. Haka kuma ya ci kwallo goma ga Portugal a wasanni tara da ya buga a 2023.

TRT Afrika

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...