Sanatocin Najeriya gaba dayansu 109, sun ba da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna bisa kuskure.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince su ba da albashin nasu a matsayin gudun mawar ga mutanen Tudun Biri da ke Karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
Read also: Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Read also: “Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
Sanata Barau Jibril wanda ya yi bayani a yayin ziyarar ta su a fadar gwamnatin Kaduna ya ce sun kai ziyarar ne domin jajanta wa Gwamna Uba Sani kan tsautsayin da ya faru a satin da ya gabata, ya bayyana cewa albashin sanatocin gaba daya ya kama Naira miliyan 109. Ya ce hakika sun yi bakin ciki bisa abin da ya faru gami da addu’a ga wadanda suka mutu da fatan Allah ya bawa wadanda suka jikata lafiya.
Gwamna Jihar Kaduna Uba Sani shi ne ya tarbi babbar tawagar sanatocin a gidan gwamnati da ke Kaduna.




























