Wani Lauya mai zaman kan sa a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ya buƙaci Shugaban hukumar Hisba na jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ya daina faɗar ayyukan hukumar da suke buƙatar sirri a gurin da bai kamata ba.
Lauya Sunusi Umar Sadiq, ya yi kiran a ranar juma’a ta kan shafinsa na Facebook kamar yadda Jaridar Inda Ranka ta ruwaito.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Barista Umar ya ce “Na kusa da Sheikh Daurawa ya kamata su faɗa ma sa duk wani abu da ya san sirri ne, ya kamata ya sani a matsayinsa na kwamandan Hisba ba dai-dai ba ne ya riƙa faɗa a wurin karatu ko kuma a ko wane yanayi da doka ba ta ba da izinin yin haka ba.”
Read also: Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanonin Dala Food Nig da POP Cola
Haka kuma Barista Sunusi, ya ƙara da cewa, “In ya na so Jama’a su san me Hisba ke ciki to su rika samar da bayyanai na shekara (annual report) ko makamancin haka wanda in jama’a na bukatar sai su nema”.
“In ka na so a yi dai-dai, dole ne kai ma ka yi dai-dai.” In ji Sunusi Umar Sadiq.




























