A ci gaba da namijin kokarin da yake wajen ganin an fito da sababbin hanyoyin da za’a taimaki al’umma domin samin ilimin Kiwon lafiya, sabon Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jahar Kano, Dr. Abubakar Umar Farouk, ya bayyana cewa Kwalejin ta shirya tsaf domin fara gabatar da darussan da suka shafi fannin Kiwon lafiya (Health Science Certificate Programs) daga zangon karatun da muke ciki na 2023/2024.
Shugaban ya bayyana hakan a yayin da yake kaddamar da kwamitin da zasu jagoranci lalubo hanyoyin da za abi don ganin an fara shirin cikin nasara a karkashin jagoranci Daraktan lura da tsare-tsaren darussa (Academic Planning), Dr. Ibrahim Usman Aikawa.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Ya Kuma bayyana cewa, “abin yana matukar damuna idan naga matasa suna yawo a gari ba tare da wata kwakkwarar sana’a ba”. Inji Dr Farouk.
Shugaban ya tabbatar da cewa, Kwalejin nada dukkanin kayan aiki gami da kwararrun malaman da za su iya baiwa dumbin matasamsu Ilimi a fannonin Kiwon lafiya tare da basu shaida (Certificate) da zasu Iya amfani da shi wajen dogaro da kansu tare da bada gudummawa a cikin al’umma.




























