Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

An Karrama Karamar Ministar Babban Birni Taraya Abuja Dr. Mariya Bunkure

Dr. Bunkure
Dr. Bunkure

Zabbabun Kansilolin na Karamar Hukumar Bunkure da Gidauniyar kiwan lafiya sun karrama Karamar Ministar Babban birnin taraya Abuja Dr. Mariya Mahmoud Bunkure bisa kwazonta na bunkasa rayuwar al’ummar yankin da jihar Kano baki daya.

Sun ce sun yanke shawarar baiwa Ministar lambar yabon ta Gwarzuwar Mace, bisa nagartattun halayenta na inganta rayuwar al’umma musamman Mata da matasa ta fuskar taimakon lafiya da ilimi da samar da ayyukan yi.

Kansilolin sun jaddada bukatar Ministar da kada ta gajiya wajen ire-iren ayyukan alkhairi da ta ke aiwatar wa ga al’ummar ta Bunkure da Rano da Kibiya da ma jihar kano baki daya. Sun kuma yi addu’a ga Allah domin ya kara ciyar da ita gaba bisa niyarta da ayyukan alkhairi da ta ke gabatar wa.

Lambar yabon da zababbun kansilolin karamar hukumar Bunkure suka bai wa Ministar ta hannun Babban mataimaki a gareta SA. Hon. Abba Kawu Gurjiya ta Isa Gareta a ranar talata.

Da yake jawabi a madadin Ministar, Babban mataimakin na musamman gareta Hon. Abba Kawu Gurjiya, ya godewa Kansilolin da gidauniyar kiwan lafiya bisa hangen nesan su da suka karrama Ministar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...