Jami’en Hukumar Yaki da masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC sun mamaye babban rukunin kamfanonin Dangote da ke jihar Legas.
Binciken ya fara ne a babban ofishin kamfanin da ke Legas da misalin karfe 3 na rana, a ranar Alhamis, har yanzuwa lokacin hada wannan rahoton ana ci gaba da gudanar da bincike.
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa hukumar EFCC na binciken kudaden da aka ware wa kamfanoni kimanin 52 da suka hada da Dangote Plc a lokacin mulkin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele.
“Hukumar EFCC tana binciken Dangote Plc da wasu manyan kamfanoni kusan 51. Hukumar ta gano cewa ba tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da kason ba,” inji majiyar.
Read also: Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kasancewar jami’an su a wurin.
Sai dai bai yi karin bayyani ba na dalilin zuwansu kamfanin ba.
“Zan iya tabbatar da cewa mutanenmu suna can, amma ba zan iya yin tsokaci kan dalilin kasancewarsu a wurin ba,” in ji Oyewale.
Read also: Motar Dangote Ta Kashe Mace Mai Ciki, Yaro Da Mutum Shida A Ondo
Global Tracker




























