Daga Adita
Bincike ya nuna cewa, tun lokacin da Arewa maso gabas da Arewa maso yamma suka sami kansu a rikice- rikice daban-dabam, kama daga na rikicin Boko Haram da satar mutane domin neman kudin fansa da ta’addanci; dubban rayuka da dukiya sun salwanta.
To amma duka wadannan abubuwan sun faru, wasu sun shude wasu kuma hukumomi na ta kokarin shawo kan lamarin domin magancewa.
Sai dai sau da yawa a kokarin magance wata matsalar wata kan faru, musamman idan aka ce sha’ani ya hada da Soji, na gwamna ga rawa ga yaki.
Abin da ya faru kwanan nan a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna ya taba zuciyar akasarin ‘yan Najeriya musamman Najeriya ta Arewa, inda jirgin soji ya afka wa masu taron Mauludi a wananan kauyan ba-su-ji-ba-su-gani ba, inda sama da mutum 85 suka hallaka, kuma daruruwa suka sami munana raunuka, a bisa sanarwar hukumar agaji ta kasa.
Wannan kafar sadarwa mai zaman kanta, wato “THESTENRORNEWS. COM” ta kalli yadda sojin sama suka kai hare-hare kan farar hula wadanda suka kira a bisa kuskure har lokuta goma sha shida (16), a tsawon shekaru 7 a jihohi Arewa daban-dabam a kasar nan.
Sai dai ma’abota hankali da ‘yan rajin kare hakkin dan’Adam da kungiyoyin matasa na Arewa da Malaman Musulunci da Kungiyoyin Musulunci da makamantansu na tambayar wai me ya sa wannan kuskuren ba ya faruwa a wasu bangare na kasar nan, sai a Arewa?
Don haka su ka yi Allah-wadai da kuma tir da wannan mummunar kaddara da sakaci, kamar yadda suka ambata. Hakan na zuwa ne bayan harin da jirgin soji mara matuki ya jefa “bam” a kan farar hula a kauyen Tudun Biri, a karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna, a lokacin da suke tsaka da Mauludin Annabin Muhammadu (SAW) a ranar 3 ga watan nan na Disamba.
TheSTENTORNEWS ta sami binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar, inda muka gano guraren da aka kai irin wadannan hare-hare na kuskure da lokuta da hakan ta faru, da kuma yawan fararen hular da aka hallaka sakamakon harin na soji kamar haka:
1. A ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2014 mutane 10 sun rasa ransu a Jihar Borno sakamakon harin jirgin soji.
2. A ranar 17 ga watan Janairun shekarar 2017 mutane 58 suka rasa ransu, a jihar ta Borno sakamakon harin jirgin soji.
3. A ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2018 wasu mutane 20 sun rasa ransu a Jihar Borno sakamakon harin jirgin soji.
4. A ranar 11 ga Afrilun shekarar 2019 mutane 11 aka kashe a jihar Zamfara sakamakon harin jirgin soji.
5. A ranar 2 ga Yulin shekarar 2019 mutane 13 sun rasa ransu a jihar Yobe sakamakon a harin jirgin soji.
6. A ranar 25 ga Afrilun shekarar 2021 mutane 30 sun rasa ransu a jihar Borno sakamakona harin jirgin soji.
7. A ranar 26 ga watan Satumbar 2021 mutane 9 sun rasa ransu a jihar Yobe sakamakon harin jirgin soji.
8. A ranar 26 ga watan Satumbar 2021 mutane 20 sun rasa ransu a jihar Borno sakamakon harin jirgin soji.
9. A ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2022 mutane 6 sun rasa ransu a jihar Neja sakamakon harin jirgin soji.
10. A ranar 6 ga watan Yulin shekarar 2022 mutane 12 sun mutu a jihar Katsina sakamakon harin jirgin soji.
11. a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2022 mutane 60 sun rasa ransu a jihar Zamfara sakamakon harin jirgin soji.
12. A ranar 24 ga watan Janairun shekarar 2023 mutane 18 sun rasa ransu a jihar Neja sakamakon harin jirgin soji.
13. A ranar 25 ga watan Janairun shekarar 2023 mutane 40 sun rasa ransu a jihar Nassarawa sakamakon harin jirgin soji.
14. A ranar 5 ga watan Maris din shekarar 2023 mutane 3 sun rasa ransu a jihar Kaduna sakamakon harin jirgin soji.
15. A ranar 18 ga watan Agustan shekarar 2023 mutum 1 ya rasa ransa a jihar Neja sakamakon harin jirgin soji.
16. A ranar 3 ga watan Disambar da muke ciki mutane sama da 90 aka hallaka a jihar Kaduna sakamakon harin jirgin soji.
Kar ku manta duka wadannan hare – haren wai sun faru ne bisa kuskure.
A yayin da mahankalta al’amura ke tambaya “Kuskure ko Ganganci” duba da wadannan tambayoyi:
Abin tambaya a nan, shin sojin sama Najeriya ba su da kwarewa ne?
Kuma jiragen da ake cewa ba su da matuki, to haka ake sakin su sasakai babu ragama bare linzami?
Wai Najeriya ce kasar da ta fara mallakar irin wannan jirgi? Idan ba ita kadai ba ce, me ya sa sauran kasashen ba a samun yawaitar irin wannan kuskuren?
A sanin mu, kowane aiki yana da tanadin doka da kuma hukunta duk wanda ya karya dokar, to su wadanda suke aikata ire-iren wannan kuskuren me ya sa ba a hukunta su, kuma a bayyana wa duniya irin hukuncin da aka yi musu domin na baya su hankalta?
Da akwai bukatar mahukuntan kasar nan su yi duba na tsanaki tare da daukar matakin gaggawa ga hukumomin tsaro domin kaucewa ci gaba da faruwar wadannan abubuwan takaici da kuma tozartar da kasarmu mai tsohon tarihi, da ta yi fice a fannin tsaro da makamantan su.
Haka kuma akwai bukatar Shugaban Kasar nan Bola Ahmad Tinubu ya ziyarci garin Tudun Biri domin jajantawa al’ummar yankin duk da cewa Shugaban Hafsan Sojin sama ya jajanta musu, Kuma a baya nan Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shattima ya ziyarci garin, amma hakan ba lallai ya wadatar ba, sannan a biya su diyyar wadanda suka rasu da kuma lura da lafiyar wadanda suka sami raunuka.
A nan muke rokon Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya, Ya kuma yi mana maganin rashin tsaron da ya addabe ta, tare da kawar mana da duk mai hannu a wannan lamari na rashin tsaron da kasarmu ta sami kanta katsahan domin wasu dalilai da su suka sani.
Haka kuma, muna rokon Allah da Ya karbi shahadar wadannan mutane da suka rasu tare da ba wa wadanda suka jikkata lafiya.
Read also: Horon Tukin Mota: Shugaban Karamar Hukumar fagge Salisu Masu Yayi Kira Ga Matasa Su Amfani Damar



























