Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kaduna ta ce aƙalla mutum 85 ne, kawo yanzu, aka tabbatar sun mutu a harin da aka kai kauyin Tudun Buri a jihar Kaduna.
Hukumar ta samu bayanai daga hukumomin yankin cewa tuni aka yi jana’izar mutanen da suka rasu, ana kuma ci gaba da yin bincike.
Read also: Motar Dangote Ta Kashe Mace Mai Ciki, Yaro Da Mutum Shida A Ondo
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Tun farko dai rundunar sojin saman ƙasar ta musanta hannu a kai harin.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
A jiya Litinin ne, Majalisar Dattawan Najeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo asarar rayuka masu yawa.
Harin dai ya faru ne yayin da mutanen ke tsaka da taron Mauludi da suke yi duk shekara.(BBC).




























