Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Yadda Wani Dattijo ‘Dan Shakara 60 Ya Shiga Jami’a, Ya Kammala da Sakamako Mafi Kyau

Farouk
Farouk

A wani abu da ba a saba ganin irinsa ba, wani tsoho mai kimanin shekaru 60 ya shiga jami’a bayan da ya yi ritaya daga aiki.

Mutumin mai suna Farouk Sanni, wanda tsohon ma’aikacin banki ne, ya shiga Jami’ar Ibadan ne, a inda ya karanta fannin nazarin halayyar dan Adam, wadda aka fi sani da “sociology” a Turance.

Ya kamalla karatun digiri na farko da mafi kyawun sakamako wato “first class honor.” Haka kuma shi ne dalibin mafi kwazo a ajinsu, ma’ana “best graduating student”.

Irin wannan jajircewa da aiki tukuru na wannan datijjo sun sa ya sami lambobin yabo da kyaututuka har guda takwas (8).

A wata zantawa da manema labarai, Malam Sanni ya ce ya karanci wannan fanni ne don ya fahimci dalilan da suke sa mutane suke wadansu irin dabi’u.

Kafin yin wannan digiri na farko a fannin nazarin halayyar dan Adam, Malam Sanni ya yi wani digirin na farko (wato bachelor degree) a fanni aikin akanta (ko accounting) a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife.

Bayan kamalla karatun a fanni aikin akanta, sai ya halarci Jami’ar Liverpool a Ingila a inda ya yi digiri na biyu a fanni nazari kan hulda tsakanin kasa da Kasa (international management).

Dattijon ya ce sai da ya zana jarabawar share fagen shiga jami’a (JAMB) kafin ya fara karatunsa, a daidai lokacin da dansa tuni yana jami’a, yana karantu a fanni shari’a.

A cewarsa, ba abu ne mai sauki ba mutum ya zauna a aji daya da yara sa’anun ‘ya’yansa.

“A ajinmu, wasu dalibai na kira na da ‘baba’, wasu kuma na kira na da Malan Sanni. A yayin da wasu ke cewa wannan baban dai (wato ni) ba ubansu ba ne,” in ji shi.

Da yake tsokaci a kan wannan batu, wani malami a Sashen Nazarin Halayyar Dan’Adam na Jami’ar Ibadan, Dakta Oludayo Tade, ya ce Sanni dalibi ne mai nacin karatu, a inda har kujera ya daure a gindin bishiya wacce yake zama ya yi karatu a karkashinta.

“Wani abun mamaki, ranar sallah na ga Sanni a gindin bishiya, a zaune yana karatu. Cikin raha na ce masa ranar sallar ma ba za ka huta, ka zauna da iyalanka ba? Sai kawai ya yi dariya, ya ce na saya musu komai da suke bukata don yin bikin Allah.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...