Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Dan majalisa ya aurar da marayu 100 a Kebbi

Aure
Aure

Wani ɗan majalisar wakilan Najeriya a jihar Kebbi ya aurar da ‘yan mata marayu su 100 a wajen wani ƙasaitaccen buki da aka gudanar ranar Asabar.

An ɗaura wa marayu 100 auren ne a fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Ismail Muhammad wanda ya jagoranci daurin auren.

Bukin ya ja hankalin jama’a a wannan yankin Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

An ɗaura auren ne ɗaya bayan ɗaya bayan sanar da biyan sadaki da kuma waliyan kowane ango da amarya.

Kowace ɗaya daga cikin amaren ta samu kyaurar saitin gado da kujeri da sauran kayan ɗaki da kuma AlKur’ani mai girma.

Ɗaya daga cikin amaren Hafsat Ismail Haruna ta bayyana auren a matsayin wani babban al’amari ga rayuwarta.

“Wannan ba ƙaramin gata ba ne domin ban taɓa tunanin zan yi aure nan kusa ba saboda ban san uwa da uba ba,” in ji ta.

Ɗan majalisar mai wakiltar mazabar Argungu/Augie a majalisar wakilai Hon Sani Yakubu Noma wanda ya ɗauki nauyin aurar da ‘yan matan har 100 ya ce ya san maraici domin shi maraya ne kuma wannan ne dalilin da ya sa ya jagoranci aurar da marayun.

Ɗan majalisar ya kafa kwamiti da suka jagoranci tabbatar da auren na marayu. Ya kuma ce zai ci gaba da aurar da marayun duk shekara tsawon wa’adin shekaru huɗu da zai yi a majalisar tarayya.
Angwayen amaren na cike da farin ciki baki har kunne saboda sauƙin da suka samu wajen samun abokan zaman rayuwa, abin da sai wasu sai sun yi gumi kafin su samu.

Sun kuma gode wa ɗan majalisarsu kan kyautata masu da ya yi ya aurar da su.

Sannu a hankali wannan al’adar ta aurar da mutane masu yawa a lokacin guda kuma kyauta, wadda aka fara a jihar Kano yanzu ta yi naso zuwa sauran jihohin arewacin Najeriya.

Al’ummar yankin arewa ta dauki aure cikin abubuwa mafiya muhimmanci a rayuwa amma rashin sukuni da kuma tsadarsa ke yi wa mutane da yawa tarnaki wajen taka wannan muhimmin mataki a rayuwa. (BBC)

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...