An bukaci Hakimai da Dagatai da Masu Unguwanni dake Masarautar Rano, dasu bada hadin kai da goyon baya domin sami nasarar gangamin shirin alluran riga kafin kamuwa da cututtukan kyanda da shan-inna (polio) da Kuma ta sankarar mahaifa Wanda za a fara gudanarwa nan bada jimawa ba a jihar Kano.
Mai Martaba sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa ne yayi kiran lokacin da yake jawabi ga wakilin hukumar kula da lafiya a matakin farko na jiha da ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa tare da yi masa jawabi kan shiye-shiryen hukumar na kammala kudirorinta na gabatar da Shirin riga kafin a duk fadin jihar Kano.
Read also: Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar
Mai Martaba Sarkin Rano ya kuma bayyana gamsuwar masarautar sa bisa wannan kyakkyawan kudiri na Ma’aikatar Lafiya da Kuma gwamnatin jiha bisa lura da inganta lafiyar jama’a.
Don haka Sarki Kabiru Inuwa, ya hori dukkan Hakimai da Dagatai da Masu Unguwannin dake yankin masarautar sa da su dukufa wajen wayar da kan jama’a su fito domin amsar wannan riga kafin bisa mahimmancin ta da zarar an fara gudanarwa.
Da yake jawabi, jagoran tawagar Alhaji Rabi’u Ibrahim, yace sun ziyarci fadar sarkin ne domin gabatar masa da wannan kudiri tare da Karin neman hadin kai da goyon baya don shirin ya Kai ga nasarar da ake bukata.
Read also: Ƙungiyar likitoci ta janye yajin aikin gargaɗin da ta fara
Alhaji Rabi’u ya shaidawa sarki cewa, a halin yanzu ma’aikatar lafiya ta jiha bisa kulawar hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kammala shirye-shirye don gudanar da gangamin alluran riga kafin kamuwa da cututtuka da za a gudanar kamar haka.
“Za a gudanar da rigakafin cutar Shan inna ( polio ) don karkade burbushin cutar daga 21 zuwa 25 ga watan Oktoba na wannan shekara ta 2023 .
Sai Kuma cutar Sankarar Mahaifa wace za a fara daga ranar 28 zuwa 31 ga watan Oktoba na bana”. Inji Rabiu.
Shugaba ya tabbatarwa da Maimartaba Sarki, cewa za a gudanar da riga kafin cutar kyanda ranar 18 ga watan Nabomba na wannan shekara ta 2023 duk domin baiwa yara kariya daga cutar ta kyanda Mai saurin halaka kananan yara.
Alhaji Rabi’u Ibrahim ya godewa sarakuna bisa gudunmawar da suke bayar wa wanda ya dangata da nasarorin da ake samu bisa dukkan shirye-shirye na samar da ingantaciyar lafiya ga jama’a.
Read also: Ebola Ka Iya Hadasa Ɗage Zaɓen 2027 A Najeriya
Haka Kuma a zaman fadar Mai Martaba Sarki, ya karbi bakuncin shugabanni da sauran jagororin Sabuwar Jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u karkashin jagorancin shugaban ta Farfesa Abdulrashed Garba ( vice Chancellor).
Jami’in shiyar yada labarai na Rano, Nasiru Habu Faragai, ya ruwito mana cewa Maimartaba Sarki, ya amshi bakuncin sabon Jami’in Shiyar Kungiyar Tsaro ta NCDSC mai lura da shiyar Rano Alhaji Lawan Ibrahim Baba da Kuma kungiyar mafarauta ta jiha karkashin kwamandan rudunar Alhaji Abdullahi Al-Ameen.



























