Hukumar NDLEA ta Yi Nasara Cafke miyagun Kwayoyi da Aka Boye Cikin Kujerun Zama da Hulunan Mata da Aka Shigo da su Najeriya
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wani babban lodin miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin kayayyakin daki da aka shigo da su ƙasar nan, musamman kujerun sofa da hulunan mata na gargajiya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, ya ce wannan na daga cikin sabbin nasarorin da jami’an hukumar suka samu.
Ya kuma fitar da bidiyoyi da ke nuna yadda aka gano miyagun ƙwayoyin.
A cikin bidiyon, an ga jami’an NDLEA suna buɗe manyan akwatunan kwali da aka shirya kujerun sofa a ciki. Bayan cire marufin waje da sosuna da ke cikin kujerun, jami’an sun gano sunki da dama na miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye a cikinsu.
A wani samame makamancin haka, jami’an sun binciki hulunan mata na ado, inda suka yanke kayan da ke rufe da su tare da gano wasu kunshin na miyagun ƙwayoyi da aka ɗinke ko Aka ɓoye a cikin kayan.
A wani ɓangare na bidiyon, an nuna layuka na buhunan da aka rufe sosai, waɗanda ke ɗauke da busasshen ganyen da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne, bayan an kwato su.
Wannan Kamu na daga Cikin babbar nasara da hukumar NDLEA ta samu na yaƙi da ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi, waɗanda ke amfani da kayayyakin yau da kullum da kayan amfanin mutane wajen ɓoye miyagun ƙwayoyi domin shigo da su Najeriya ko fitar da su zuwa wasu ƙasashen waje.
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
A shekarun baya, hukumar ta sha gano irin waɗannan hanyoyin ɓoye miyagun ƙwayoyi a cikin kayan daki, huluna, takalma, kayan lantarki da sauran kayayyakin da ake shigowa da su ko fitarwa ta tashoshin ruwa ko filayen jiragen sama da kamfanonin jigilar kaya.
Wannan na nuna yadda masu safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙirƙirar sabbin dabaru domin guje wa jami’an tsaro.




























