Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Ƙungiyar PTA First Lady College Ta Yi Allah-Wadai Da Bikin ‘Candy’ Ta Buƙaci Ɗaukin Gwamnati

PTA First lady college
PTA First lady college

Ƙungiyar PTA First Lady College Ta Yi Allah-Wadai Da Bikin ‘Candy’ Ta Buƙaci Ɗaukin Gwamnati

Daga Wakilan Mu

Ƙungiyar Iyaye da Malamai na makarantar (PTA), First Lady College ta yi tur da Allah-wadai da murnar ‘Candy’ da ɗalibai kan yi a duk lokacin da suka kammala jarabawar fita da ga makarantun Sakandire.

Mataimakin Shugaban Ƙungiyar, Ni’imatullahi Bashir Saed, shi ya sanar da haka da yake faɗakar da ɗaliban makarantar dake dab da kammala jarabawar su ta ƙasa a dakin taro na makarantar a yau Alhamis.

Ya ce an shirya taron ne domin faɗakar da ɗaliban da za su kammala karatu kan muhimmancin kauce wa duk wani abu da zai iya bata sunan makaranta da iyayensu ko kuma ya zubar musu da daraja, musamman kasancewar su mata iyayen al’umma.

Gwamnatin Kano Ta Rufe Film House Da Ke Unguwar Dorayi, Mutane na Sambarka

Ni’imatullahi wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar reshen makarantar, ya gargaɗi ɗaliban da su kaucewa wannan mummunar dabi’a wace babu ita a addini ko al’adar Bahaushe.
Don haka ya ce makarantar ba za tai ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar duk matakin da ya kamata domin hukunta duk wace ta yi wanna rashin da’a.

Ya kuma yi kira ga iyaye su ci gaba da sanya ido kan ‘ya’yansu tare da ba su tarbiyya mai nagarta domin su zama shugabanni na gari a nan gaba.

Da yake jawabi Mai binciken Kuɗi (Auditor ) na ƙungiyar, Malam Mu’azam Aminu Gezawa, ya ce bikin ‘Candy’ ya sabawa ka’ida kuma baya cikin tsarin ilimi, addini ko al’adar Bahaushe.
Ya ce daga cikin abubuwan da ake yawan aikatawa yayin bikin ‘Candy’ akwai yaga kayan makaranta, rubuce-rubuce a jikin unifom, kaɗe-kaɗe, hawa saman gine-gine, hayaniya da kuma Farfesa kayayyakin makaranta gami da cin zarafin ɗalibai da malamai.

” Kai bilhasali ma wannan biki babu komai a cikinsa sai fasadi da barna, kuma yin hakan shi ke jawo fushin Allah domin an aikata abun da basu dace ba”, in ji Malam Aminu Gezawa.

JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya

Ya ce duk ɗalibar da take so Allah yasa albarka a karatun ta, ta kaucewa fushin Allah Subhanahu Wata’ala.

Malam Aminu ya kuma kira ga gwamnati da ta fito da hanyoyin magance bikin ‘Candy’ da kuma hukunta masu kunna ƙashi.

A nata ɓangaren, Shugabar Makarantar First Lady College, Hajiya Atine Muhammad, ta yabawa Ƙungiyar Iyaye da Malamai bisa fadakar wa, tana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tarbiyya da kuma tunasar da ɗaliban ƙalubalen da ke gaban su bayan kammala makarantar.

Ta ce wannan shine karo na farko da aka shirya irin wannan taron tun bayan kafuwar makarantar, inda ta bayyana fatan cewa zai taimaka wajen rage ayyukan rashin ɗa’a da wasu ɗalibai ke aikatawa bayan kammala jarabawar ƙarshe.

Hajiya Atine ta kuma gode wa Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano bisa goyon bayan da ta ke bai wa makarantar, tare da kira ga sauran ƙungiyoyin iyaye da malamai su yi koyi da irin wannan shiri domin inganta tarbiyya da ɗabi’u a tsakanin ɗalibai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...