Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Huɗuba: Babu Dabara Ka Ɓoye Kayyan Masarufi, Kuma Ka Biya wa Wasu Aikin Umarah, In Ji Liman Nura Ishaq

Babban Limamin Masallacin Juma'a na Hisbah, Nura Wada Ishaq
Babban Limamin Masallacin Juma'a na Hisbah, Nura Wada Ishaq

Huɗuba: Babu Dabara Ka Ɓoye Kayyan Masarufi, Kuma Ka Biya wa Wasu Aikin Umarah, In Ji Liman Nura Ishaq

Daga Sunusi K/Naisa

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hisbah a ƙaramar Hukumar Gwale Malam Nura Wada Ishaq, ya ce babu dabara ga musulmi ya azabtar da ‘yan uwa ta hanyar ɓoye abinci ko sinadari da rayu ke ta’allaka da ita, kuma daga bisani ya biya wa wasu aikin Umrah ko yake basu sadakar kunu da makamantansu.

Limamin ya bayyana haka a huɗubarsa ta Juma’a a yau, ya ce Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hani da zalunci gami da azabtar da ɗan adam musamman Musulmi.

Malam Nura Ishaq, ya ja hankalin masu wadata da yan kasuwa a cikin al’umma da su sauƙaƙa wa musulmi ta sassauta kayan masarufi domin samun rahamar Allah maɗaukakin Sarki.

” Babu basira ka gallazawa al’ummar Annabi ta hanyar tsawalawa a dukkanin abin da ka ke saidawa, da ga bisani kuma ka sai abinci ko biyawa wasu Umar, in da ya ce ko kusa Allah baya rahama ga masu zalunci”. In ji Liman Nura.

Malamin ya kawo ayoyi daga Alkur’ani mai Tsarki da Hadisan Annabin Rahama da su kai bayanin rankon azabar da za ayi wa mai ɓoye abinci da makamantan su a ranar lahira ga dukkanin masu aikata hakan.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su kauce wa mummunar aƙidar ƙin ɗaukar azumi ko sauke wa bayan an sanar da ganin watan Ramadan ko kuma watan Shawal.

Babban Limamin ya rufe huɗubar da addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya yi wa musulmi maganin masifar da ke addabar ƙasa da jihar Kano baki ɗaya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...