Gwamnan Abba Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin 2026, na zambar N1.368 tiriliyan
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da daftarin kasafin kudin jihar na shekarar 2026 Wanda ya kai adadin N1,368,127,929,271 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Yayin da yake jawabin a gaban Majalisar dokokin jihar Kano gwamnan ya nanata kudirin gwamnatinsa na kammala manyan ayyukan da gwamnatisa ta gada domin cigaba al’umma.
Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanonin Dala Food Nig da POP Cola
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa manema labarai.
Ya ce an warewa manyan aiyuka kaso mafi yawa daga kasafin kudin, wanda ya kai N934.6 biliyan. Sai kuma kashi 32 cikin ɗari na kuɗaɗen gudanarwa da suka kai Naira bilinyan N433.4
Gwamna Yusuf ya ce fannin Ilimi ya samu kaso mafi tsoka na N405.3 biliyan (30%), sai ayyukan raya ƙasa da aka ware musu Naira N346.2 biliyan (25%), sannan bangaren lafiya aka ware masa Naira N212.2 biliyan (16%).
“Wannan kasafin ya nuna aniyar mu ta ci gaba da gina ɗan Adam, ta hanyar inganta ilimi da lafiyar jama’a, tare da shimfida tubalin cigaba mai ɗorewa a jihar,” in ji Gwamna.
Ya ce ɓangaren tattalin arziki da walwalar Jama’a su ne suka fi samun kaso mai yawa na daftarin kasafin na 2026, waɗanda suka haɗar da Noma, Tsaro, Kasuwanci, Ruwa, Muhalli, yawon bude ido, ci gaban mata da matasa, da kuma kula da masu buƙata ta musamman.
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
Maniyata aikin Umara daga Indiya mutum 42 sun mutu sakamakon hatsarin mota a Saudia
Ya bukaci ’yan majalisar da su hanzarta amincewa da ƙudirin kasafin, domin a fara aiwatar da shi akan lokaci don cigaban jihar Kano .




























