Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Hanyar Dan Madanho ta gagari Kundila, mazauna yankin na roƙon Gwmna Abba ya kawo ɗauki

Dan madanho
Dan madanho

Hanyar Dan Madanho ta gagari Kundila, mazauna yankin na roƙon Gwmna Abba ya kawo ɗauki

Daga Sunusi K/Na’isa

Mazauna garin Dan Madanho da ke ƙaramar hukumar Gezawa sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu ɗauki cikin hanzari tun kafin garin ya ƙulle.

Mazauna yankin sun nemi gwamnatin da ta share musu hawaye ne bisa magance matsalar hanyar Dan Madanho zuwa garin Zango wacce take ci musu tuwo a kwarya shekara da shekaru, a wata ganawa da jami’in yaɗa labarai na shiyyar Gezawa, Jamilu Mustapha Yakasai ya yi da su.
’yan yankin sun bayyana irin mawuyacin halin da hanyar ke ciki tare da yin kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki cikin gaggawa domin sauƙaƙa matsalolin sufuri da kuma fita daga halin ni ‘yasu.
A Iya Karanta Wanna:Yarjejeniyar Zaman Lafiya da Alero: Gaskiya Ko Wasan Kwaikwayo Da Rayukan Al’umma
Kamar yadda suka nunar sun sha kai kokensu ga karamar hukumar Gezawa domin a gyara mummunar hanyar da ta hada al’ummarsu da Zango dama wasu sassa makwabta amma hakan ya citura, don haka suke miƙa kokensu ga Gwmna jiha mai kishin al’umma Abba Kabir Yusuf da ya dube su da idon rahama musamman ganin damina ta gabatowa.
Al’ummar yankin waɗanda suka nuna gamsuwa da jindaɗinsu kan cigaban da mai girma Gwamna Abba Kabir yake samarwa a Kano musamman a fannin kiwon lafiya, ilimi, gina hanyoyi a sauran sassa a faɗin jihar nan.

Da yake magana kan mahimmancin hanyar, Dattijo, Alhaji Isah Dan Madanho, ya bayyana muhimmancin ta wanda yafi gaban misaltuwa a fannin tattalin arziki da lafiya. Ya bayyana cewa, hanyar ta haɗa al’ummomi da dama, kuma da zarar an gina ta, za ta bunƙasa harkokin tattalin arzikin yankin gami da kyautata rayuwar jama’a baki ɗaya.

Da yake ƙarin haske, shugaban ƙaramar hukumar Gezawa, Alhaji Mukaddas Bala Jogana, ya ce ginin hanyar aiki ne na gwamnatin jiha kuma yana bibiyar ma’aikatar ayyuka ta jiha a ƙarƙashin kwamishinan Ayyuka domin ganin an fara aikin hanyar nan bada jimawa ba.

Ya kuma bukaci al’ummar yankin da su kasance masu haƙuri da fatan alheri, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba za a fara aikin titin Dan Madanho.
A Iya Karanta Wanna:Iftula’i: Barayin Waya Sun Kashe Wani Haziƙin Ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da marawa manufofin gwamnati da tsare-tsaren ta na cigaba da nufin ɗaukaka martabar jihar Kano.

Binciken da jaridar The STENTOR NEWS online tayi, idan har aka gyara wanna hanya mazauna garin da makwabtanta kamar Zang da Bala da Babawa da Bangare da kuma Tsalle zasu sami sauƙin zirga-zirga ma’amula ta yau da kullum.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...