DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2)
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)
Idan ba a manta ba muna kan tattaunawa akan abubuwan da ake bukata lokachin (Brooding) ɗin kaji, to inshallah zamu dora daga inda muka tsaya.
MAGUNGUNA DA RIGAKAFI
Matukar kana kiwo to ya zama wajibi gareka ka samar da magunguna, muhimmai a ciki su ne ‘Antibiotic’ da ‘Vitamins’ (Ana amfani dasu wajen yaqar kwayoyin cuta da kuma kara wa garkuwar jiki kwari) waɗannan magunguna guda biyu(2) indai anyi amfani dasu yadda ya kamata to har mai kiwo ya gama kiwonsa ba lallai ya nemi wasu ba domin cutar ma bazata samu damar bulla ba.

‘Yan tsaki
Har wa yau akwai wasu magungunan da suke da muhimmaci ga mai-kiwo ya ajiye wanda suka haɗar da na cutar (COCCIDIOSIS, NEWCASTLE) da kuma na magani KWARI saboda duk waɗannan cutuka ne masu haɗari da lokaci guda suke kawar da kaji duk yawansu, a kwai na gargajiya da ake amfani dasu wajen samar da maganin wanda sabon mai kiwo babu bukatar ya fara aiki dasu tukunna (Organic medication) Inshallah zan tattauna hakan a gaba.
Ka Iya Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
Rigakafi dai ana yinsa kafin cuta ta kama kaji ba bayan ta kamsu ba, domin kaucewa barkewar annobar cutar. , Manyan Rigakafi da akafi yiwa kaji sune ‘GUMBORO da LASOTA‘ wanda ake yin ɗaya a satin farko dayan kuma sati na biyu, idan ba dole ba to babu bukatar a sake yi musu wata Rigakafi har sanda za a fitar dasu.
Read also: DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
Kamar yadda da yawa masu kiwo suka sani yawancin rigakafi suna zuwa a fannin Kwaya da ake sanyawa a ruwan shan kajin domin su sha ko kuma ta hanyar Allura. Amma an fi amfani da hanyar sanya musu a ruwa domin ita tafi sauki kuma ta ke basu damar shan ruwan a wurin cikin hanzarin.
* TSABTA
A nan idan muka ce tsabta, muna nufin ta muhallin kajinka, a akurki suke (cage) ko a cikin daki kai ko kwali suke, suna da matukar buƙatar ka tsabtace musu muhallinsu domin kare su daga cutuka wanda zasu iya samuwa ta dalilin kazantar da wurin ke dashi.
Kazantar da wurin kiwo ke dashi yana haifar da wani wari mai ƙarfi wanda ‘ammonia’ ke samar wa ta dalilin Kashinsu, haka kuma kazantar kan cutar da kaji musamman ta hanyar girman su don tana dakile girman kaji wato su tsumbure, cutuka irinsu ‘COCCIDIOSIS da NEWCASTLE‘ suna saurin yaduwa a muhallin kaji mai kazanta.
Ka Iya Karanta Wanna:Boko Haram: Zulum ya bayar da gudummawar N30m ga iyalan hafsan sojojin da aka kashe, Alari
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Inshallah zamu ɗora daga inda muka tsaya na ‘kiwan kaji a lokacin sanyi’. Mu haɗu a kashi na uku.
Daga Yazid Sunusi Yahaya, dake unguwar Kofar Nai’sa a jihar Kano, Nijeriya.
#stentornews
#yazeedpoultryfarmer
#eachoneteachone




























