Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)
Sau da dama mutane masu kiwon kaji kan samu damuwa zarar lokacin sanyi ya karato ballantana idan a shiga muku-mukun sanyin na hunturu. Hakan na faruwa ne bisa cututtukan da ke kama kaji waɗanda ke da alaka da mura da kuma cutar numfashi.
A bisa yawaicin lokaci hakan kan jawo mutuwar wasu daga cikin kajin ko ma gaba dayansu. A saboda haka na ga yuwar yin bincike game da kiwan kaji a lokacin sanyi irin na hunturu kuma ba tare da tafka asarar ba.
Wani abokina na gwagwarmaya wato Hayatu Rufa’i Hayatu, ya bani labarin fara kiwonsa amma a cikin sanyi har yake neman shawara domin kaucewa asarar. Alhamdulillah! wanna shi ya bani tunanin yin wannan rubutun, kuma na raba rubutun zuwa gida goma (10) domin bawa ‘yan uwa masu kiwo irina shawara da kuma sanin dabarun kiwan a wanna yanayin domin suma su amfana.
Ka Iya Karanta Wanna:Sojoji Sun Lakume Manyan Kwamandojin Bello Turji Guda 7, Da Sauran Yaransa 24
Kaɗan daga cikin hanyoyin da za ka bi ko za ki bi don cimma buri na samar da lafiyayu kuma kosassun kaji ba tare da an samu mutuwar kajin da yawa ba, ko ma gaba ɗayan su, wato (zero mortality).
Read also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2)
BROODING ( Raino): Da farko ka kula da abunda ake kira BROODING, toh! wani zai iya cewa menene (Brooding), shine kulawar da ake bawa kaji tun suna ƙanana wato (Day old) ko ‘yan tsawon sati ɗaya ko sati biyu (7-14 days) a killattaccen wuri domin samun ingantacciyar kulawa kamar yadda zasu samu daga mahaifiyarsu (Kaza) duk da cewa waɗanan ‘yan tsakin na Nasara ba su da Uwa, domin kyankyasar inji ne.
A lokacin (Brooding) ana samar da abubuwa kamar haka:-
* DUMI KO ZAFI : Ta hanyar samar da Kwan lantarki musamman Ja da sanya mu su garwashi, ko Kuma duk wani hanya da zai samar da dimi a inda suke, tare da kiyaye wa da ka’idar sanya dumin wanda ba a so ya wuce 35’C wato ma’uni sanyi. Wani zai iya cewa ni bana gane wannan ‘C ba, haka ne, tun da kalmace ta Bature, toh! akwai hanyar da ake bi kamar Haka:
– A duk sanda kaga kajinka sun takure wuri ɗaya har takai da wasu na danne wasu to suna buƙatar ‘Dumi’ ke nan, ma’ana wurin yayi sanyi da yawa kuma za iya cutar da lafiyar su.

‘Yan tsaki
– A duk sanda kuma bayan ka sanya musu ‘Dumin’ sai ta kasance sun yi nesa da ‘Dumin’ ma’ana sun je ƙarshen keji (cage) ko dakin kiwonsu, hakan na nufin zafin yayi musu yawa.
Amma idan bayan ka sanya musu ‘Dimi’ kuma kaga suna dara da tsalle tare da wani kuka mai sanya nishadi musamman idan ka zuba musu dusa to tabbas, yana tabbatar maka kajinka suna Jin dadin dumin kuma yayi musu dai-dai. Duk da shi wannan dumin akwai kalar dusar da idan kana bawa kajinka itama tana samar musu da dimi. Amma idan munzo bangaren kalar abincin kaji zan maka/ku bayani anan gaba inshallah.
Ka Iya Karanta Wanna:Horon Tukin Mota: Shugaban Karamar Hukumar fagge Salisu Masu Yayi Kira Ga Matasa Su Amfani Damar
Read also: Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet
* HASKE : Kaji musamman (Day old) suna bukatar Haske 24/7 ma’ana kowane lokaci tsawon kwana bakwai ko 14 na “brooding”, amfanin haske shine don basu dama su ci abinchi a wannan lokacin na raino (brooding), anan ana nufin abinci mai yawa sosai wato su ci abinci su sha ruwa su huta sai su ci gaba da wannan zagayen a inda aka samar musu.
Mu haɗu a rubutu na gaba.
Za a iya samun Yazid Sunusi Yahaya a No.652 Lokon Makera, Kofar Naisa WhatsApp: 09098150359 Call: 09131853295




























